Babi Na Farko

Màu nền
Font chữ
Font size
Chiều cao dòng

***

An hanzarta daukar mahaifiyata, Hajiya Zainab Akorede zuwa Asibiti. Ina tare da ita, ina karanta addu'ar datazo min a hankali. Zuciyarta tana bugawa a raunane matuƙa, tana shakar numfashi da taimakon na'urar oxygen. Mama bata dawo cikin hayyacin ta ba tun sanda Al'amarin ya auku. Bana son taso da maganar a yanzu saboda kwanaki biyar  da  Suka shud'e sune mafi munin kwanaki a rayuwata....
Kamar yadda yake, an sallame ni daga wannan Asibitin  mintina da suka wuce. Ina tare da mama acikin "Dakin Emergency" muna jiran likita ya cire alburushin daga gefen goshin ta na dama saboda yana fitar da jini.

Malam shehu,Ustaz luqman tare da mahaifina, Imam Hussain Muhammad suna tare da likitan.

"karki kara zuwa inda mum take, mahaukaciya, mayya!"
Ibrahim, yayana ya shigo cikin ward din ya janye ni daga wurin mama da karfi.

"ke kika sanya ta cikin wannan yanayin sannan kuma kike addu'a?! 'yan fashin sunyi miki fyad'e ne dalilin ked'in mara sa' a ce, bana so in 'kara ganinki kusa da mama, kawai ki wuce gida kuma ki bace mana da gani!"

'yaya... "na kira sunanshi a sanyaye yayin da 'kwalla me daci take taruwa a ido na.

" ki fita a rayuwar mu tare da wannan shegen 'Dan naki, mun gaji da masifar da hakan take jawomana!"ya furta cikin 'karaji da fushi.

" yaushe zaka dena aikata wannan zunubin? Ka dena wannan sumbatun , yaya ibro! Ba laifi na bane, ko me zakayi kuwa... Don haka kar ka ajiye tsanar ka a kaina saboda nima ban ta'ba son hakan ya faru dani ba. "na furta da rawar murya yayinda nake matsawa gab dashi, tare da 'Daura hannuna na dama akan kafadarsa, amma seya hanzarta janyewa da karfi.

" yaya Ibro, ina imaninka yake? Hawayen bakin ciki suka sauko daga gajiyayyun idanuwa na. Zuciya ta, murya ta har jikina rawa suke yi sosai. Can 'kasan zuciyata, nasan cewa bazan ta'ba komawa kamar 'Aisha Akorede' d'in da nake a kwanaki biyar din da suka wuce ba.

"Allah ya fad'a cewa mu yarda da kaddara me kyau da mara kyau." Na cigaba. "Muna ƙoƙarin shiryawa kanmu abinda ya dace damu, amma Allah shine mafi sani akan abinda ya dace damu, kayi imani da Allah komai zai daidaita Insha Allah...." na fuskance shi tare da sanya idanuwana cikin jajayen idanuwansa... Babu Abinda nake iya hangowa acikinsu se tsananin bacin rai da tsana.

" Amma baki da hankali gaskiya, Aisha! Kin haukace! Nakasa yarda wai har kece kike iya fadamin hakan a halin yanzu!tsayuwar ki anan tana ba'kanta min rai, ki 'bacemin da gani... Hajiya, tsarkakakkiya!!!" Ya jamin tsaki cikeda kyamata,ya fice ya barni Ina Hawaye.

***

Babana sun fito daga ofis ɗin likita tare da abokan sa, Imam Hussain da kuma wasu dattawa. Ina shirin Barin ward din da mama take nayi tozali dasu babana. Alamun firgici  da wahala kwance baro-baro a fuskokinsu amma abinda yake fuskar baba yafi tsoratani. Cikin hanzari na karasa wajenshi.

Baba... Baba, meke faruwa ne?! Mama zata warke kuwa?! Baba, kace wani Abu mana... Ina ro'kon ka karka yi min shiru haka, shirun ka yana matuƙar tsoratani! "ina magana wasu sabbin 'kwalla suna taruwa a idanuwa na.

Baba ya ruko fuskata a hankali, yana kokarin kirkirar murmushi amma hakan ma ya gagara.

'yata, likita yace maman ku tana buƙatar aiki cikin gaggawa a 'kwa'kwalwar ta, indai har muna bukatar ta rayu. Matsalar da muke fuskanta a yanzu shine.... 'Kwararren likitan da zaiyi aikin baya gari. Baze samu shigowa ba se wajen jibi".

"ya Allah! Abin babu daɗin ji Sam, amma baba yanzu ya zamuyi?"

"muna ta shirye shiryen fitar da ita ƙasar waje, amma bamu da isashshen kuɗi da kuma lokaci. Likitan yace idan munyi sauri za'a iya samun ta.

Muna tsaye Ibrahim ya tako inda muke tsaye ya Dam'ki hannuna.

" Aisha! Idan mama ta rasu, tabbas sekin bita".

Jikina yayi sanyi sosai, yadda kaina da zuciyata suke ciwo a yanzu ya zarce ciwon da jikina keyi.

Bana yad'an turashi baya.

"Ibrahim, kayiwa mutane shiru! Badai a gaban manya kake yin hakan ba. Ka dinga kai zuciya nesa, ka dena furtawa 'kanwar ka irin waɗannan kalaman! Kamata yayi ka dinga tausaya Mata, ka zama me share Mata hawaye, ba ka dinga kyararta ba hakanan!"

"Baba ka barni na koyawa yarinyar nan hankali!"

Ya juyo dani ina fuskantar sa.

"Dama bakya raye a yanzu haka! Dama baki dawo ba kin mutu can,tare da shegen danki!"

"Ibrahim, ka dena wannan sumbatun haka, kana kunyata kanka!"

"Aisha, kin ga abinda kika jawo ko? Baba ya tsaneni saboda ke! Duk laifin ki ne, kuma zan ɗauki mummunan mataki akan ki, kar ki damu!" Ya hankad'e ni tare da ficewa daga Asibitin cikin matuƙar sauri.

"Ibrahim!, ka tsaya ka tafi da 'kanwar ka gida. Da kai fa nake magana, kar ka kuskura ka fice ina maka magana.... I-B-R-A-H-I-M!!"
Baba ne yake kiransa da iya karfin muryarsa amma ibro ko juyowa bai yai ba.

"Yaa Allah!! Yaa Rahman!!! Ohh Allah, ka ji'ban ci al'amurana. Allah kai kaɗai ne me zartarwa, Kai kaɗai ne me ji, Allah ka amsa Addu'a ta..." Wasu zafafan hawaye suka sauko saman fuskata,duk da hakan ina ƙoƙarin boyesu da Ɗan ragowar jarumtar data rage min.

"Baba, ina ro'kon ka. Ka tuna da shekarun da kake kyawawan aiyuka, sadaukarwa da jihadi. Na ro'ke ka, kar ka bari wata damuwa ta girgiza imaninka, kayi 'ko'kari hakan ya kara maka imani. Baba! Kaine ka koyar dani yin 'ko'kari da takatsantsan da sanin wacece ni a kowane yanayi na tsinci kaina. "Na goge ragowar hawayen fuskata, tare da ru'ko hannayensa na haɗa da nawa." Baba, ka koyamin miƙa lamarina tare da sanya Allah a farko duk abinda nasa a gaba, hakan zesa nayi nasara. Kaine majingina ta, kuma kaine me karfafa min gwiwa, karka juyamin baya a yanzu danake da tsananin bu'katarku kamar yadda Ibrahim yayimin...." Na rungumeshi da duk karfina ina kuma fashewa da matsanancin kuka.

" ya isa hakanan, Aisha. Don Allah ki daina kukannan haka, zaki 'karawa kanki damuwa ne kawai."
Ya janyeni daga jikinsa a hankali tare da taimaka min na zauna, akan wata farar kujerar roba acikin reception din.

"Maman ku..... Likitan yace zata iya rasa ranta nanda Awa ashirin da huɗu. Aisha, maman ku tana cikin mawuyacin hali gashi 'Kwararren likitan bezo ba haryan zu."ya girgiza kansa daya hada gumi cikin rashin sanin abinyi.
" canza Mata Asibiti ko kuma tafiya da ita wani wuri ze iya zama hatsari, na rasa yadda zanyi. "

" Baba, Allah yana nan, Allah yana tare damu akoda yaushe, yana amsa addu'o'in mu. Allah me ji ne, kuma yana kallon komai, ina imaninka yake, kar mu karaya a wannan gaɓar, kada imaninmu yayi rauni. Ka manta? Idan har Annabi yusuf AS ya dawowa mahaifin sa Annabi yakub AS. Insha Allah nayi imani Mama zata dawo gareni, babana. "Na d'ago ina kallon fuskar babana, na kafe gajiyayyun idanuwan sa na d'an lokaci. Nima ina tare da damuwar rashin sanin abinyi kusan ma daidai da nashi damuwar,wacce ta kasa boyuwa a fuskarsa.

Kamar na tuna wani Abu a lokacin dana ambaci Sunan annabawan Allah AS.

"Baba, ka jirani anan, zanje na dawo yanzu." Na fice daga  harabar Asibitin da gudu ina neman inda zan ga masallaci.

"yauwa! Na furta tare da sauke ajiyar zuciya lokacin dana hango wani karamin masallaci da farin fenti a hanyar fita daga Asibitin, nayi hanzarin isa wurin fanfo amma ba ruwa. Na duba drums, bokitai da butoci suma duk babu ruwan.Nayi kokarin hada ragowar ruwan butoci kusan 7 amma ba zasu isheni ba Sam.

Cikin sauri na fita can wajen Asibitin Don siyen pure water a wani gidan abinci dake kallon Asibitin. Nadawo ciki, na d'auro alwala tare dayin nafila raka'ah biyu. Zama nayi na fara tilawar wasu daga cikin ayoyin alkur'ani cikin tawakkali da gusar da tsoron da yake zuciyata.

Mamallakin sammai da kassai, idan kayi nufin wani Abu, se kace kasance,! Hakan kuma seya kasance(Q2: 117)

Ya Allah kaji 'kan iyaye na, kamar yadda suka tausayamin  ina jariri (Q17:24)

"Ya Allah,ya mafi girman iko, ka turo 'kwararren likita ya duba mahaifiyata,Ya me jin tausayin bayinsa, ya me girma, ka ceto mahaifiyata daga mutuwa a wannan yanayi, ka kare iyalina daga sharrin shaidan da waswasinsa, da duk wani mugu dayake saka mugunta a zuciyar dan Adam. Ya Allah ina ro'kon ka, ka kare mahaifiyata daga mutuwa ta wannan hanyar, Ya Allah ka amsa addu'ata ka tashi mahaifiyata... Kamar yadda ka amsawa nana zulaiha  addu'ata. "

***
Mintuna kadan da suka shude.

Nadawo cikin ward d'in ina karanta suratul-nass a hankali, izuwa yanzu nasan na karanta yakai sau d'ari.Muna zaune kawai naga likita ya dafa kafadar mahaifina sannan yace. ;

" Alhaji, 'kwararren likitan ya 'karaso, ya makara jirgi ya tafi ya barshi, ya fasa tafiyar."

"Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar kabirah!" ɗaya daga cikin abokan babana, ustaz lukman ya dinga kabbara da ƙarfi.

An shigar da mama d'akin tiyatar cikin gaggawa. Hankulan mu sun fara kwanciya, tiyatar zata dyauki kusan awa uku.

Na fito na hau taxi Don komawa gida don in kintsa, ina zuwa na tarar da Ibrahim a 'kofar gidan yana Tara icce da karare, ya d'auko file d'ina Wanda yake ɗauke da dukkanin muhimman takardu na aciki.

"Assalamu Alaikum, babban yaya." na gaisheshi da maɗaukakin murmushi shimfid'e akan fuskata. "Huh-huh, yayana na kaina! Ashe dawowa kayi da wuri don ka gyara mana gidan kafin isowata." na kalle shi cikin lumshe idanuwana, amma seya maida min kallon da wani malalacin murmushinsa na mugunta.

"Ehh, inata jiran dawowar ki. Saboda kiga lalacewar ki da idanuwan ki."

"Me kake nufi da lalacewata kuma? Wai wadannan kerosene ne da ashana a kusa da kai?"Na tambaya ina kyalkyalewa da dariya.
" Idan Allah yaso ka 'kona takardun nan, yaya ibro. Da tuni ka 'kona su, bazaka jira isowata ba Sam. "

" Haba? " Ya tambaye ni a d'an firgice. Naga alamar wuyan ki yayi kauri."

"Na tabbatar indai har ina nan wurin ba zaka ta'ba kunna wuta akan takardunnan ba." Na shige cikin gidan Don ajiye ledar hannuna na barin shi a tsaye yayi  duk abinda yaga dama.

Yana shirin zuba kerosene d'in akai, Ɗanlami yayi ihu da ƙarfi.

"Ƙaramin megida, ina cikin girki.... Kai! Girkina ne ya 'kone kurmus! Hayaki ya cika ko ina a d'akina wayyo! wayyo! wayyo!!! Kai!!!

" Ya Ilahi!"Ibrahim ya furta a tsorace ya bi me aikin da gudu cikin kitchen domin dubo abinda yake faruwa.

Naje na ɗauke file dina, sabo fil babu abinda ya sameshi nayi masa kyakkyawar ajiya.Duk abubuwan da suke faruwa dani a wannan lokacin kara tabarbarewa sukeyi, ina jin kamar zuciyata bazata iya d'auka ba nan gaba kad'an. Bayan nayi sallar la'asar, senayi shawarar zuwa gidansu aminiyata tun yarinta, Adunni ikudaisi. Ina tafe inata maimaita wannan addu'ar  acikin zuciyata.

"Rabbanaa 'aatinaa  min-ladunka rahama tan waa hayyi' lana min amrina rashadaa. (Q18:V10)."






Bạn đang đọc truyện trên: Truyen2U.Pro